Daga Abba Ibrahim Wada Gwale

 

Mai tsaron ragar kungiyar kwallon afa ta Juventus, Gianlugi Buffon ya bayyana cewa zuciyar alkalin wasa Machael Oliver, wanda yayi alkalancin wasan da suka buga da Real Madrid babu komai aciki kuma  tazama kwandon shara.

 

Buffon dai an bashi jan kati a wasan bayan da ya nuna rashin jin dadinsa da hukuncin da alkalin wasan ya yanke a wasan inda alkalin wasan yayi zargin ya tureshi  sakamakon ya bawa Real Madrid bugun fanareti.

 

Mai tsaron ragar yaci gaba da cewa yakamata alkalin wasan yayi aiki da hankali sannan kuma ya dinga fahimtar lokutan daya kamata ace ya dauki wasu hukunce-hukunce sannan kuma ya lura da girman wasan da kuma lokacin da ake buga wasan.

 

Ya kara da cewa yakamata ace Machael Oliver yana saman bene yana kallon wasan tare da yan uwansa da abokansa sannan kuma yanacin biskit ga Coca Cola yana sha.

 

A karshe yace alkalin wasan bashi da zuciya ko kadan kuma zuciyarsa kamar kwandon shara take sannan kuma yabawa alkalan wasa kunya.

 

Real Madrid dai yanzu takai wasan kusa dana karshe bayan data doke Juventus daci 4-3 a wasanni biyu da suka fafata gida da waje.

 

LEAVE A REPLY