Lakosa

ZANYI FARIN CIKI IDAN NAJERIYA TA TAFI DANI GASAR CIN KOFIN DUNIYA – IN JI JUNIOR LAKOSA

Daga: Abba Ibrahim Wada Gwale

Dan wasan gaba na kungiyar kwallon kafa ta kano Pillars, Junior Lakosa, wanda kawo yanzu yafi kowanne dan wasa zura kwallo a raga a gasar firimiyar Najeriya da kwallaye 14 yace zaiyi farin ciki sosai idan Super Eagles ta Najeriya ta gayyace shi zuwa gasar cin kofin duniya a kasar Rasha.

Lakosa ya bayyana hakane a hirarsa da manema labarai inda yace zaiyi alfahari idan yasamu wannan damar ta wakiltar kasar nan a gasar da babu kamarta a duniya kuma yana fatan hakan.

Yaci gaba da cewa abin alfahari ne ace yabuga wasa da shahararrun yan wasan Super Eagles din kuma idan har an gayyace shi zai bada gudunmawar data dace domin ganin kasar ta samu abinda yakamata.

A tsakiyar kakar wasan data gabata ne dai dan wasa Lakosa yakoma Kano Pillars daga kungiyar First Bank dake jihar Legas inda acikin wasannin daya buga a iya lokacin ya zura kwallaye biyar.

Ya kara da cewa gogewa da inda yakamata ace dan wasan gaba yana zuwa da kuma taimakon yan wasan kungiyar Kano Pillars ne yasa yake samun nasarar zura kwallo a raga a wannan kakar sannan ya kara da cewa yan wasan kungiyar sun bashi dama kuma suna taimaka masa sosai kuma yana aiki tukuru domin ganin ya bunkasa wasanninsa.

LEAVE A REPLY