'Yan Kungiyar Kwallon kafa ta Barcelona suna murnar samun Nasara

Karawar manyan kungiyoyin kwallon Sifaniya, wato Barcelona da Madrid ta haifar da zazzafar Muhawara a ko ina, sakamakon cin Ala-tsine uwar mai karya da Barcelona ta yiwa Madrid din.

An dai jima ana yiwa juna kallon hadarin kaji tsakanin kungiyar kwallon kafa ta Barcelona da abokiyar burminta ta Real Madrid, musamman a wannan wasan El-Classico da aka buga a ranar Asabar.

Magoya bayan kungiyar kwallon kafa ta Barcelona sun barke da sowa da ihu, bayan da kungiyar kwallon tasu ta yiwa Madrid ci uku ba ko daya.

Dan wasan gaba na Barcelona, Suarez shi ne ya fara bude zaren Madrid din da wata kwallo da ya antaya musu jimkadan da dawo daga hutun rabin lokaci.

Bayan da gumu tayi gumu tsakanin Barcelona da Madrid ne, dan wasan Madrid yayi makuwa, inda ya nemi tare kwallon da aka so zura musu da hannu, nan take alkalin wasan ya baiwa Barcelona damar bugun tazara na daga kai sai gola.

Samun wannan dama, Barcelona ta baiwa Leonal Messi damar wannan bugu, inda ya dankara ta a ragar Madrid, abinda ya mayar da wasan ci buyi da nema.

Ana sauran mintuna kadan a hura tashi, dan wasan Barcelona Vidal ya sake zura kwallo ta uku a ragar Madrid.

Anga magoya bayan Barcelona na murna hade da shewa a ko ina, yayin da na Madrid suka yi fuskar shanu.

LEAVE A REPLY