Arsen Wenger

Daga Abba Ibrahim Wada Gwale

Mai koyar da yan wasan Arsenal, Arsene Wenger, yace, zai bar qungiyar a qarshen kakar bana, bayan da ya shafe kusan shekara 22 a qungiyar

Mai koyarwar, xan qasar Faransa, zai bar qungiyar ne shekara xaya kafin sabuwar kwantiraginsa ta zo qarshe.

Qungiyar dai ta Arsenal itace ta shida a teburin firimiya kuma akwai yiwuwar ba za su samu damar zuwa gasar Zakarun turai ta baxi.

Wenger, mai shekara 68, ya ci wa qungiyar Kofin gasar firimiya sau uku da kofin qalubale na FA bakwai, da suka haxa da waxanda ya xauka a lokaci xaya a shekarun 1998 da 2002.

Yaceya ji daxin samun damar jan ragamar qungiyar na tsawon wasu shekaru da ba zai manta ba kuma yana fatan qungiyar zata cigaba da samun nasara a wasanninsu na gaba.

Yace ya ja ragamar qungiyar da dukkan azama da mutunci sannan yace yana kira ga duk masoyan Arsenal, su kula da mutuncin kungiyar sai dai yace Zasu kawo qarin bayani nan ba da jimawa ba.

LEAVE A REPLY