Sergio Ramos

Daga Abba Ibrahim Wada Gwale

Rahotanni sun bayyana cewa watakila hukumar kwallon kafa ta nahiyar turai ta sake dakatar da dan wasan baya na kungiyar kwallon kafa ta Real Madrid, Sergio Ramos, bayan da dan wasan ya sakko kusa da inda masu horarwa suke duk da cewa an dakatar dashi daga buga wasan.

Ramos dai an dakatar dashi daga buga wasanne bayan yasamu katin gargadi a wancan wasan da aka fafata a kasar italiya sai dai an hango shi yana kusa da masu horarwa da ragowar yan wasan kungiyar kuma har yayi cacar baki da mai koyar da yan wasan Juventus, Maximilliano Allegri akan bugun fanaretin da aka bawa Real Madrid.

Laifin da yayi ya sabawa dokar kwallon kafa shashi na 15 da yace ba’a yarda dan wasa ya saka kansa ba acikin abinda yake faruwa ba a wasa idan har an dakatar da dan wasan.

Alkalin wasa, Mikel Oliver, zai kai rahoton wasan a yau kuma idan har yakai da laifin na Ramos za’a sake dakatar dashi wasa daya kamar yadda yake a doke.

A shekara ta 2014 lokacin da Real Madrid ta doke Atletico Madrid a wasan karshe bayan da Gareth Bale ya jefa kwallo Xavi Alonso ya shigo fili ya taya yan wasan kungiyar murna duk da cewa baya buga wasan saboda an dakatar dashi amma daga baya sai da aka hukunta shi aka hanashi buga wasa a shekara ta gaba.

LEAVE A REPLY