Daga Anas Saminu Jaen

A ranar Asabar 2 ga watan Disamba, 2017 aka kammala gasar wasan langa na cin kofin Ibrahim Galadima shugaban hukumar wasanni ta jihar Kano tsakanin ‘yan wasan Zuma da Jarumai, a wani yinkurin su na dawo da sada zumunci tsakankanin unguwanni da farfado da al’adun gargajiya na dauri.

An yi wannan wasan ne a harabar makarantar Firamaren Zawaciki a yankin karamar hukumar Kumbotso ta jihar Kano. An kammala wasan, wanda Jarumai ta zo ta biyu da maki 1 inda Zuma ta zo ta farko da maki 3 wanda ko wannen su ya samu kyauta.

Wasan Langa: langa wasa ne na gargajiya na musamman a kasar Hausa. Wasa ne da aka dade ana yin sa shekaru aru-aru, wasa ne da aka fi sanin  matasa ‘yan kasa da shekaru 20 da suke yi a lokacin da suke ke jin nishadi a wuraren dandalin su na wasanni, wannan wasa, birni da kauye ko ina ana yin sa. Mafi yawanci, kuma, matasa sukan gudanar da wasan ne da dare idan sun ci abinci sun koshi, wato bayan sallar Isha’i.

Kamar yadda aka gudanar da wasan na ranar Asabar, kowane gari sun sanya alamar shiga gasar domin banbanta gari, a gargajyance dai ana gudanar da wasan langa ne tsakanin mutane biyu ko fiye da haka, ya dangata da adadin matasan da ke wasan. Yadda ake gudanar da langa; ‘yan wasan langa sukan lankwashe kafarsu ne a bayan su, su rike babban yatsan su da hannu ko dai kafar hagu ko ta dama suna tafiya da kafa daya, daga nan sai su fara kai wa juna hari ta hanyar turewa duk wanda ya fadi sai ya yi gefe.

A tsarin wasan Langa, da aka gudanar  a Zawaci ‘yan wasa 16 ne suka kara, kowane gida ‘yan wasa 8 ne kuma wasan akan zabi gida daya su yi “Ruwa” wanda shi ake turewa idan kuma yakai wurin shedar da aka yi shi ne ya ci, wannan wasan langar ya hada dubban mutane sassa daban-daban na makoftan filin da aka yi wasa maza yara da manya tare da manyan baki da suka halarta.

Haka dai aka gudanar da wasan tsahon kimanin sa’o’i biyu da rabi cikin farin ciki da annashuwa wanda aka kammala tsakin masu sada zumuncin biyu Zuma da Jarumai, wasan ya samu halartar ‘yan jaridu da jami’an tsaron ‘yan sanda masu kaki da na farin kaya wanda aka kammala wasa lafiya ya mai wasa da micijin tsumma ‘yan wasa lafiya ‘yan kallo lafiya.

LEAVE A REPLY