Daga Hassan Y.A. Malik

Dan wasab tsakiya na Manchester United, Pau Pogba, ya yi karin haske kan rade-raden da ya cika kafafen yada labarai na batun tsamin da dangantakarsa ta yi da kocinsa, Jose Mourinho.

Pogba ya bayyana cewa babu wata matsala ko tsamin dangantaka tsakaninsa da Mourihon duk kuwa da ajiye shii a benchi da kocin nasa ya ke yi, ya yi amfani da matashi McTominay.

Pogba ya sake dawowa zabin farko na jerin ‘yan wasa 11 da Mourinho ya lashe wasan gasar Firimiya sati na 31 da su a ranar Asabar din da ta gabata, inda Manchester United ta lallasa Swansea da ci 2 da nema.

A ta bakin Pogba, ya ce, “Gaskiya ne ban taba fuskantar ajiyewa a benchi ba, amma ajiye ni din ya kara karfafa ni. Dole a rayuwa sai ka gamu da irin wadannan koma bayan in har kana da bukatar ka yi nasara.

Babu wata matsala tsakani na da Mourinho. Ba ni ne nake zabar wadanda za su wakilci tawagar a wasanni ba, saboda haka in kana so ka san dalilin da ya saka bana buga kowane wasa na Man Utd, sai ka tambayi koci na. Ina martaba zabinsa a koda yaushe,” Pogaba ya fadawa kafar Telefoot.

Da aka tamabayi Pogaba batun barin Man Utd a karshen kakar bana, sai dan wasan da Man Utd ta saya a shekarar 2016 akan fam miliyan 89 ya kada baki ya ce, ” Ya yi wuri na fari batun sauaya sheka a karshen kakar bana saboda komai na iya canzawa.”

LEAVE A REPLY