kungiyar kwallon kafa ta Real Madrid ta shirya kasha kudi har fam miliyan 180 domin siyan yan wasa Paulo Dybala na kungiyar kwallon kafa ta juventus da kuma Antoine Griezman na abokiyar hamayyar su wato Atletico Madrid.
Shugaban gudanarwar kungiyar ta Real Madrid, Florentino Perez dai ya shirya kasha wannan kudi ne sakamakon rashin zura kwallo a raga da kungiyar take fama dashi a wannan kakar.
An bayyana cewa yan wasa Karim Benzema da Gareth Bale sune zasu bar kungiyar domin samun shigo da Dybala da Griezmann.
Real Madrid dai tana fama da rashin zura kwallo a raga inda har yanzu dan wasa Cristiano Ronaldo kwallo daya ya zura a gasar laliga wanda hakan wani babban kalubale ne ga kungiyar sannan kuma yawan zuwa ciwo yana hana Bale da Benzema buga wasa.
Madrid din dai itace ta uku akan teburin laliga maki biyar tsakaninta da Barcelona wadda take matsayi na daya sannan tana matsayi na biyu a gasar zakarun turai a rukunin da take inda Tottenham ta kasar ingila itace take jan ragamar rukunin.
Sai dai wannan labarin bazai yiwa Manchester united dadi ba domin itace take zawarcin Griezman kusan shekara daya bayan da a kwanakin baya takusa daukar dan wasan kafin ya canja shawarar cigaba da zama a kasar sifen din.
Itama Manchester city itace take zawarcin Dybala bayan da suke tunanin shine zai maye musu gurbin Sergio Aguiro wanda ake tunanin zai bar kungiyar a karshen wannan kakar.

LEAVE A REPLY