Daga Hassan Y.A. Malik

An samu sabanin ra’ayi tsakanin fitaccen dan wasan gaba na Real Madrid, Cristiano Ronaldo, da shugaban gudanarwar kungiyar ta Real Madrid, Florentino Perez, kan wanda za a take wasa da shi tsakanin Karim Benzema da Gareth Bale a wasan karshe na cin kofin zakarun turai da kungiyar za ta kara da Liverpool a ranar 26 ga watan nan na Mayu a birnin Kiev

Karin Benzema bai wani rawar gani ba a kakar bana, inda ya kare kakar da zura kwallo 10 kacal tare da taimakawa jefa 11.

Sai dai, kafar yada labarai ta Don Balon ta rawaito cewa, Ronaldo a wani zama da ya yi da mai horas da ‘yan wasan kungiyar Zinedine Zidane da kuma kyaftin din kungiyar a makon ya zabi da a take wasa da Karim Benzema, wanda hakan ke nufin Gareth Bale ya jira a benci.

Sai dai a ra’ayin shugaban gudanarwar kungiyar ta Real Madrid, Perez ya zabi da a take wasa da Bale, a kuma bar Benzema a benci.

Dalilin Perez na lalle sai an fara da Bale bai wuce don ya farfado da darajar dan wasan ba, ta yadda zai kara kima a idon masu bukatar sayensa a kokarin kungiyar ta Madrid na sayar da Bale din bayan wasan karshe na cin kofin zakarun turan.

A nasa bangaren, kocin kungiyar, Zinedine Zidane, da aka tambaye shi game da yadda zai zabi ‘yan wasan da za su buga wannan wasa na karshe, sai ya kada baki ya ce, “Ina da ‘yan wasa 24 wanda daga cikinsu ne zan…..

“Ku gafarce ni, amma bani da wasu zabin kalmomi da suka fi abinda zan fada, amma ya zama dole na bar wasu a nan Madrid wasu kuma zan tafi da su Kiev. Wannan ita ce kalubalen da na ke fama da shi a halin yanzu.”

LEAVE A REPLY