Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari tare da Firaministar Burtaniya Theresa May

Daga Abba Ibrahim Wada Gwale

Kungiyar kwallon kafa ta Real Madrid za ta kara da kungiyar Bayern Munich a gasar cin kofin zakarun Turai yayin da Liverpool za ta kara da Roma wadda tayi waje da Barcelona a gasar.

A yau ne hukumar kula da kwallon kafar nahiyar turai ta raba kungiyoyin hudu da suka rage a gasar bayan kungiyoyin sun samu nasara a wasannin da suka buga na kusa dana kusa dana karshe.

Za a yi wasannin a ranakun 24/25 na watan  nan na Afrilu, sai zagaye na biyu a ranakun 1/2 ga watan Mayu mai zuwa kuma a watanne za’a buga wasan karshe.

Za a buga wasan karshe na gasar zakarun Turai a birnin Kiev, na Ukraine, ranar 26 ga watan Mayu.

Real Madrid ta fitar da Juventus a wasan dab da na kusa dana karshe, yayin da Roma ta fitar da Barcelona.

Ita kuwa Liverpool ta doke Manchester City, sai Bayern da ta yi waje da Sevilla ta kasar sipaniya a wasanni biyun da suka fafata

A bara ma Real Madrid, wacce ke rike da kanbun, ta fitar da Bayern a kan hanyarta ta lashe gasar sai dai Bayern Munchen na kokarin lashe gasar a karon farko tun shekara ta 2013.

Bayern ce za ta fara karbar bakuncin wasan farko, yayin da Roma za ta ziyarci Liverpool a wasan farko.

LEAVE A REPLY