Daga Abba Ibrahim Gwada Gwale

Fitaccen dan wasan Real Madrid kuma zakaran kwallon duniya da ya lashe kyautar Ballon d’Or a bara Cristiano Ronaldo, ya bukaci kungiyar ta taimaka ta biya masa tarar da Ofishin haraji na Sipaniya ya kakaba masa.

A bara ne dai Sipaniya din ta yi ikirarin cewa Ronaldon dan Portugal mai shekaru 33 ya damfareta ta hanyar kin biyanta wasu kudaden haraji da yawansu ya kai dala miliyan 13, ta hanyar hada baki da wani kamfani wanda ke boye yawan kudaden da ya ke samu.

Matukar dai Ronaldon baya fatan zaman gidan kaso to fa dole ne ya biya gwamnatin Sipaniya Yuro miliyan 30 wanda kuma tun tuni Ronaldon ke neman Real Madrid ta biya masa amma ta yi kememe da batun.

Yanzu haka dai Ronaldon wanda ke matsayin na biyu a xaukar kuxi a fagen tamaula bayan takwaransa na Barcelona Lionel Messi, yana xaukar dala dubu 340 kowanne mako.

Ko a bara ma dai sai da fitaccen dan wasan kwallon kafar nan dan kasar Argentina ya yi ta shiga kotu sakamakon kaucewa biyan haraji ga gwamnatin ta Sipaniya wadda ta ce ya hada baki da mahaifinsa wajen kaucewa biyan harajin ko da ya ke Messin ya ce ba da saninsa ba ne domin yana cike takardu da yawa matakin kenan da ke hana shi karantawa don fahimtar takamaiman abin da ke cikinsu.

Sipaniya dai ta yankewa Messin hukuncin daurin kusan shekaru 2 a gidan kaso yayinda ta yankewa mahaifinsa hukuncin watanni 15 ko da dai an sauya hukuncin zuwa tara daga bisani.

LEAVE A REPLY