Golan liverpool, Karius

Daga Abba Ibrahim Gwale

Mai tsaron ragar kungiyar kwallon kafa ta Liverpool, Lucas Karius, dan kasar Jamus ya nemi afuwar kungiyar da magoya bayanta bayan yayi kuskure a kwallaye biyu da kungiyar Real Madrid ta zura a ragar Liverpool a wasan karshen da suka buga ranar Asabar.

kwallo ta farko da mai tsaron yaja aka zura a ragar kungiyar tasa itace ta farko wadda Karim Benzema ya zura a raga sai kuma kwallo ta biyu wadda Bale ya buga daga nesa kuma taje wajen mai tsaron ragar amma kuma yakasa tare kwallon.

Karius yace ranar Asabar ranar bakin ciki ce a rayuwarsa domin shine yasa basu samu nasara ba a wasan sakamkon kura kuran daya tafka kuma yasan kowa baiji dadin abinda yafaru ba musamman magoya bayan kungiyar.

An hango mai tsaron ragar dai yana bawa magoya bayan kungiyar hakuri a filin wasan sakamakon kuskuren nasa kuma wasu daga cikin magoya bayan kungiyar sun amshi hakurin nasa ta hanyar daga masa hannu.

Karius yace yan wasan kungiyar dai basuji dadin abinda yafaru ba amma kuma basu nuna masa ba kawai dai suna bashi hakuri ne suna karfafa masa gwuiwa amma kuma yasan suma basuji dadi ba.

Wannan dai shine karo na 13 da kungiyar ta lashe kofin kuma karo na uku a jere yayinda kuma wannan wasan na karshe shine wanda Liverpool ta buga bayan shekaru 13 batare da tazo wasan karshe ba.

 

LEAVE A REPLY