Hassan Y. A. Malik

Tsohon dan wasan kungiyar Liverpool da tawagar kwallon kafa ta Ingila, Steven Gerrard ya yabawa  Mohamed Salah bisa kwallon mai kyau da ya zura a ragar FC Porto a karawar da suka yi a daren Laraba, inda Liverpool ta lallasa Porto da ci 5 da nema a gasar cin zakarun turai, rukunin kungiyoyi 16.

Sai dai kuma, Gerrard ya ja kunnen magoya bayan kungiyar Liverpool da su kaucewa kwatanta Salah da Lionel Messi.

Mai horaswa, jurgen Klopp ya hada Salah, Mane da Firmino a gaba, a matsayin wadanda za su zura kwallo a ragar abokan karawarsu. Hakan ya yi tasiri matuka, kasancewar su ukun ne suka zura kwallaye 5 da Liverpool ta durawa Porto.

Zuwa yanzu dai Salah na da kwallaye 30 a dukkan gasannin da ya wakilci kungiyarsa ta Liverpool a bana.

Gerrard ya ce: “hadakar Mane, Salah da Firmino ya yi kyau matuka, domin a duk lokacin da suka hari abokan karawa, akwai yiwuwar kwallo za ta iya shiga raga. Amma ba daidai bane a kwatanta Salah da Messi.”

LEAVE A REPLY