Daga Abba Ibrahim Wada Gwale

Kungiyar Paris St-Germain ta kasar Faransa ta dauki kofin gasar kasar Faransa, na Ligue 1 bayan da ta lallasa masu rike da kofin Monaco 7-1 a filin ta na Parc des Princes dake babban birnin kasar.

Yadda ‘yan wasan kungiyar mallakar Qatar suka nuna iyawa da bajinta ya sa suka yi wannan nasara ta yankan shakku wadda ta sa suka ba wa Monaco ta biyu a tebur tazarar maki 17, kafin kammala gasar da wasa biyar.

Giovani lo Celso da Angel di Maria kowanne ya ci bibbiyu, yayin da Edinson Cavani da Julian Draxler kowa ya saka xaixai a raga.

Dan wasa Radamel Falcao na Monaco shi ya ci kansu ta bakwai din, yayin da Rony Lopes ya ci musu ladan-gabe, guda daya a wasan da za a ce bangare daya ne ya yi rawar-gani.

Kofin shi ne na biyar na gasar ta Faransa, da PSG ta ci a cikin kaka shida datake buagawa tun bayan da Qatar suka karbi ragamar jagorancin kungiyar.

Monaco ta dauki kofinta na farko ne a cikin shekara 17 a kakar 2016-17, bisa jagoranci ko kokarin Falcao da kuma zuwan matashin kan wasan Faransa Kylian Mbappe.

Falcao ya ci gaba da zama a Monaco, amma Mbappe wanda ya koma PSG a kan fam miliyan 166, farko a yarjejeniyar aro, da kuma wasu manyan ‘yan wasan kamar dan baya Benjamin Mendy sun bar kungiyar a bazarar da ta wuce.

Wannan tafiya ta tarin gwanayen ‘yan wasan ta raunana Monaco wadda ita ce mafi karfi cikin abokan hamayyar PSG.

Wannan ne ya sa kusan a ce ba makawa kungiyar ta PSG  za ta sake zama zakara a Faransa saboda duk da haka itama ta siyi sababbin yan kwallo.

PSG ta doke Monaco 3-0 a wasan karshe na cin kofin kalubale na lig na Faransa ( French League Cup), a karshen watan da ya gabata, sai kuma ga shi a wannan karon lallasawar ta ma fi waccan.

 

LEAVE A REPLY