Daga Hassan Y.A. Malik

Dan wasan gaba na PSG, Neymar Junior ya bayyana yadda ya aikin da aka yi masa a sawunsa ke kara samun sauki gabanin gasar cin kofin duniya ta shekarar 2018 da za buga a kasar Rasha.

Dan wasn mai shekaru 26 da ya samu raunin karaya a tsintsiyar yatsun kafarsa tun ranar 25 ga watan Fabrairu a karawar PSG da Marseille a gasar cin kofin manyan kungiyoyin kwallon kafa na kasar Faransa ya yi magana da manema labarai a birnin Sao Paulo ta Braziliya.

“Likitoci za su yi min dubawa ta karshe a ranar 17 ga watan Mayu, kuma daga wannan dubawar zan iya taka leda.”

“Likitoci sun duba ni makon da ya gabata kuma sun ce ina samun sauki kamar yadda ya kamata, saboda haka ina fata saukin ya ci gaba da samuwa ta yadda zan dawo wasa nan ba da jimawa ba.”

“Ina samun kulawar likita a kowace rana, saboda haka da zarar na fara atisaye zai mayar da hankali sosai wajen ganin na samun karfin jiki ta yadda za samu buga gasar cin kofin duniya da na yi shekaru 4 ina jiran zuwansa.” inji Neymar

LEAVE A REPLY