Daga Hassan Y.A. Malik

Dan wasan kungiyar kwallon kafa ta Barcelona kuma kyaftin din kasar Ajentina, Lionel Messi, a yanzu haka shi ne dan wasan da ya fi kowane dan kwallon kafa a duniya samun kudi ta hanyoyin albashinsa da garabasa daga kungiyarsa da kasarsa da kuma talluka da ya ke yi kamfanoni.

Wannan sabon batu na kunshe ne a mujallar kwallon kafa ta kasar Faransa mai suna France Football Magazine.

Messi ya buge takwaransa na Real Madrid da kasar Fotugal, Cristiano Ronaldo, wanda a bara shi ne wanda ya fi kowane dan kwallon kafa samu, inda kudin shigar Ronaldo a bara ya kama: Yuro miliyan 87.5 a shekara, shi kuma Messi ke samun yuro miliyan 76.5 a shekara.

Sai dai a bana, Messi ya yi wa Ronaldo fintinkau, inda ya ke samun yuro miliyan 126, shi kuma Ronaldo ya ke samun yuro miliyan 94.>

Ga jerin ‘yan wasa biyar da suka fi samun kudin shiga a bana:

1. Lionel Messi (ARG/Barcelona): €126m
2. Cristiano Ronaldo (POR/Real Madrid: €94m
3. Neymar (BRA/Paris Saint-Germain): €81.5m
4. Gareth Bale (WAL/Real Madrid): €44m
5. Gerard Pique (ESP/Barcelona): €29m

LEAVE A REPLY