Daga Abba Ibrahim Wada Gwale

‘Yan wasan kungiyar kwallon kafa ta Panathinaikos na kasar Girka sun fara yajin aiki saboda ba a biya su albashinsu na bara ba.

‘Yan kwallon, wadanda suke jiran a biya su kudadensu na Disamba amma aka gaza yin hakan a shekarar 2018, sun fara yajin aikin ranar Litinin.

Sai dai kungiyar ta  shaida wa manema labarai cewa za a biya ‘yan wasan kudadensu na watan Disamba ranar Alhamis kuma ana sa ran su dawo atisaye.

Ana sa ran wasan da za su kara na Super League da Atromitos zai gudana kamar yadda aka tsara ba kamar yadda ake rade radin cewa baza’ayi wasan ba saboda yan wasan suna yajin aiki.

Panathinaikos, wadanda suka lashe gasar Lig ta Girka sau 20, su ne na tara a teburin gasar ta bana kuma an bayyana rashin albashin ne yasa yan wasan kungiyar basa kokari.

A makon da ya gabata, an kwace musu maki uku saboda sun kasa biyan tsohon ‘dan wasan baya na Jamus Jens Wemmer bashin da ya ke binsu.

A makon da ya gabata, an ci tarar ‘yan wasan Olympiakos Yuro 400,000 sannan shugaban kulob din ya neme su da su tafi hutu saboda rashin taka rawar gani.

Hakazalika a watan da ya gabata, an dakatar da shugaban Paok Salonika na shekara uku bayan da ya shigo fili da bindiga a lokacin da suke buga wasa da AEK Athens.

LEAVE A REPLY