Kociyan Asinal, Arsen Wenger

 

Hassan Y.A. Malik

‘Yan wasan tawagar kwallon kafa ta Arsenal sun gudanar da wani taro ba tare da kocin kungiyar Arsene wenger ba, inda kafatanin ‘yan wasan suka aminta da cewa Wenger(n) ba zai iya ciyar da kungiyar gaba ba.

Mujallar UK Guardian ta rawaito cewa, wani jigo a cikin ‘yan wasan na Arsenal ya gabatar da wani jawabi mai tsuma zuciya a wajen taron, inda a cikin jawabin nasa ya ke cewa har ‘ya’yansa na kokawa da yadda kungiyar ta Arsenal ta yi matukar lalacewa.

An jiyo wani cikin ‘yan wasan na Arsenal na cewa, “Kungiyarmu babbar kungiya ce, amma magana da ta gaskiya muna bukatar agaji daga masu horas da mu.”

Wani dan wasan har lau ya bayyana ra’ayinsa cikin fushi, inda ya ke cewa, “Sam haka ba za ta sabu ba, dole ne mu nemawa kanmu mafita da kanmu.”

Wannan dai na zuwa ne bayan da kungiyar Manchester City ta lallasa Arsenal din sau biyu a jere da ci 3 da nema a kowane wasa; na farko a wasan karshe na gasar Carabao Cup a ranar Lahadin da ta gabata, sai kuma wasan gasar firimiya da suka buga a ranar Alhamis din da ta gabata.

Akwai yiwuwar hukumomi a Arsenal za su duba batun kawo karshen zaman Wenger a Arsenal a karshen kakar bana.

LEAVE A REPLY