Olivier Giroud

Daga Abba Wada Gwale

Ɗan wasan gaba na ƙungiyar Arsenal, Olivier Giroud, ya zura ƙwallonsa ta ɗari a tarihin zamansa ƙungiyar bayan da ya zura ƙwallo ɗaya a wasan da Arsenal din ta lallasa Bate Borrisov da ci 4-2 a gasar Europa da su ka fafata a ranar Alhamis.

Giroud, ɗan shekara 30 wanda ya koma Arsenal daga ƙungiyar Montpellier ta ƙasar Faransa, ya bi sahun ɗan wasa Thiery Henry da Ian Wright da Cliff Bastin a sahun wadanda su ka zura ƙwallaye 100 a ƙungiyar.

Ɗan wasan wanda ɗan asalin ƙasar faransa ne, ya kusa barin Arsenal a kasuwar siye da siyarwa ta watan Agusta bayan da ƙungiyar ta siyo Alexandre Lacazatte shi ma daga ƙungiyar Lyon ta Faransa inda kungiyar Westham ta ingila ta yi zawarcin sa.

A wasan da Arsenal ta buga Theo Walcott ne ya zura ƙwallo biyu a raga.

Bisa ga dukkan alamu ƙungiyar farfado daga yanayin da ta shiga na rashin kataɓus, inda ta yi sa’ar doke Bate Boristov a wasan Europa.

Wasan da suka tashi 4-2, ranar Laraba, ya kasance na biyu da Arsenal ta ci a rukuninsu na takwas (Group H) na gasar kofin Turai ta Europa.

Walcott ya fara zura wallo a raga ne a minti na tara da shiga fili, sannan ya ƙara ta biyu a minti na 22.

Rob Holding ya ci wa Arsenal kwallonsa ta farko a minti na 25, wadda ta kasance ta uku ga kungiyar, kafin kuma Giroud shi ma ya ci tasa a minti na 49 da bugun fanareti, kwallon da ta kasance ta 100 da ya ci wa ƙungiyar.

Bate ta samu ƙwallayenta ne ta hannun Ivanic a minti na 28 da shiga fili, yayin da a minti na 67 Gordeychuk ya ci musu ta biyu.

Arsenal ce ƙungiya ta farko da ta doke Bate a gida a wata cikin gasar kofin Turai, tun bayan da Barcelona ta ci ta a wasan rukuni na kofin zakarun Turai a 2015- a wasa bakwai kenan.

Arsenal ce ta ɗaya yanzu a rukunin da maki shida, yayin da Red Star Belgrade ta ke zaman ta biyu da maki hudu, bayan da ta ci Cologne, wadda ta sha kashi a wasanninta biyu, da ɗaya mai ban haushi.

LEAVE A REPLY