Gambo Muhammad

Daga Abba ibrahim Wada Gwale

 

Ɗan wasan gaba na ƙungiyar ƙwallon ƙafa ta Kano Pillars, Gambo Muhammad, ya bar ƙungiyar ta Kano Pillars zuwa ƙungiyar ƙwallon ƙafa ta Rivers United da ke garin Fatakwal.

Shekarar Gambo goma a Kano Pillars kuma ya taimakawa ƙungiyar ta lashe kofin Firimiya na ƙasa sau hudu sannan ƙungiyar ta je wasan kusa da na ƙarshe na gasar cin kofin zakarun nahiyar Africa.

“Nabar Kano Pillars bayan sama da shekaru goma da na yi a ƙungiyar kuma nabar kulob din ne saboda yanzu baya buƙatar wasa na kamar yadda suka sanar dani,” inji Gambo.

Dan wasan dai ya koma Kano Pillars ne daga ƙungiyar ƙwallon ƙafa ta Buffalo shekaru goma da suka gabata.

Ya ci gaba da cewa: “Kano garina ne, anan aka haifeni na girma kuma zanyi kewar magoya baya da kuma ƙungiyar da na zama kyaftin dinta shekaru biyu da suka gabata.”

Gambo ya ce abin farinciki ne bugawa Kano Pillars wasa kuma ya kasance wanda yafi kowanne dan wasa zura ƙwallo a tarihin ƙungiyar.

Sannan ya ce ya samu gayyata daga ƙungiyoyi daban daban ciki da wajen ƙasar nan amma abu mafi sauki shine komawa Rivers United domin ita ce zaɓinsa duk da cewa zai sha wahala komawa Jihar Rivers da zama, amma haka zai zauna kuma zai saba da yanayin garin.

Ya ƙara da cewa “Da hawaye a cikin idanuwana ina yiwa kowa a ƙungiyar fatan alheri da magoya baya da mutanen Jihar Kano gaba daya.”

Gambo Muhammad dai ya wakilci yan wasan Najeriya a kofin Confederation wanda akayi a ƙasar Brazil a shekara ta 2013, kuma ya buga wasan da Najeriya ta sha kashi a hannun ƙasar Sifaaniya da ci uku babu ko daya.

LEAVE A REPLY