Daag Hassan Y.A. Malik

A yau Asabar, 10 ga watan Maris ne za a kara tsakanin kungiyoyin Burtaniyan nan da suka dade suna adawa da juna, wato Manchester United da Liverpool.

Za a yi wannan haduwa ne a gidan Manchester United, wato Old Trafford da karfe 1:30 na rana agogon Nijeriya.

Sai dai rahotanni na nuna cewa watakila dan wasan tsakiya na Manchester United, Paul Pogba ba zai buga wasan na yau ba sakamakon wata ‘yar tangarda da ya samu a na cikin atisaye a jiya Juma’a.

Jami’an lafiya na Manchester United sun ce za a yi wa dan wasan gwaji na karshe a safiyar yau Asabar wanda shi ne zai tabbatar ko Pogba zai iya buga wasan ko a’a.

Masu sharhin wasannin sun bayyana cewa in har Pogba bai bugawa wasan na yau ba, to, lalle zai zamewa Man Utd tangardar da zai iya sawa su yi rashin nasara a wasan na yau.

Man Utd dai ita ce ta biyu a teburin Firimiyar Ingila, inda ta ke saman Liverpool da maki biyu kacal

LEAVE A REPLY