Antonio Conte

 

Hassan Y.A. Malik

Kocin Chelsea, Antonio Conte ya bayyana cewa kungiyar da ya ke jagoranta`ta Chelsea ta yi rashin nasara a hannun takwararta ta Manchester City da ci 1 da nema a wasan da suka buga a yau Lahadi a wasan gasar Firimiya na mako na 29 ne saboda sun buga wasa ne da kungiya da ke ji da kwarrarun ‘yan wasa masu nagarta kuma wadanda ke cikin yanayi mai kyau dalilin kasancewarsu a can saman teburin gasar ta firimiya.

Conte ya ce mun fara wasan da nutsuwa da kuma taka tsan-tsan ta yadda hanzarinmu ba zai haifar mana da gibi a tsakakkanin ‘yan wasanmu ba ta yadda Man Ciy za su yi amfani da damar gibin su yi mana illa.

Abubuwa na tafiya kamar yadda muka tsara, amma kawai sai muka yi rashin nasara Man City ta jefa mana kwallo sakan 30 da dawowa daga hutun rabin lokaci, wanda wannan shi ne ya yi dalilin sauyawar yanayin wasan.

“Yana da matukar wahala ka buga wasa da tawagar da ta ke samanka da maki 25 kuma ta ke da ‘yan wasan masu nagarta. A wannan yanayi dole ka buga wasa da kwakwalwarka ba da kokon kanka ba,” inji Conte.

Chelsea dai ita ce ta biyar a kan tebur, inda ta ke bin Tottenham da maki 5 da ragowar wasanni 9 a kammala gasar Firimiya ta bana.

LEAVE A REPLY