Koc din Arsenal Wenger

Daga Hassan Y.A. Malik

Kocin Arsenal, Arsene Wenger ya bayyana dalilin da ya sanya kungiyarsa ta sha kashi a hannun takwarrarta ta Manchester United da ci 2 da 1 a wasan da suka buga jiya Lahadi na gasar Firimiya mako na 36.

Dan wasan tsakiyana na Manchester United, Paul Pogba ne ya bude cin kwallo a minti 16 da soma wasa, sai dai kuma a minti na 51 tsohon dan wasan Manchester United, Henrikh Mkhitaryan ya farke wa Arsenal.

Sai dai Marouane Fellaini ya jefa kwallon da ta zama yanke hukunci a minti karshe na wasan, dalilin da ya sanya Manchester United ta samu nasarar komawa da foyint 3 gida.

Wenger ya bayyana dalilin rashin nasarar Arsenal a matsayin gajiya da ‘yan wasansa suka yi, bayan da rashin gogewa da suke da shi, dalilin da ya sanya natsuwarsu ta gushe, suka kasa daukar hura musu wutar da abokan karawarsu na Man Utd suke yi musu.

“Tawagarmu na cike da ‘yan wasa masu karancin shekaru. Sun yi rawar gani matuka, amma wannan bai sanya na caccake su a dakin shiryawa ba bayan an kammala wasan saboda sai da suka gama duk wata bajinta da ya kamata a ce sun yi kuma kawai sai suka bari aka jefa mana kwallo a nmintin karshe.”

“An yi ta jefa wasu tambayoyi kafin wasan namu, inda a ka dinga cewa shin muna da karfin da za mu iya tunkarar Manchester United? Dole na ce mun nuna jajircewa, mun buga wasa mai kyau, kuma mun kara da Man Utd bamu bari sun bi ta kanmu ba. ‘Yan wasanmu da dama sun nuna bajinta a matsayinsu na daidaikun ‘yan wasa.”

“Sai dai ‘yan wasanmu sun gajiya a minti 20 kafin a kammala wasa, inda muka yi ta sakin balabalan da a minti 70 na farko bamu saki ba. Wannan dole ya jefamu cikin samun rashin nutsuwa, inda suka ‘yan wasan Man Utd suka yi amfana da wannan damar wajen jefa mna kwalo a mintin karshe.”

“It was negative result but a positive performance. Unfortunately that happens.”

“Wasa ne da zan iya bayyana shi a wasa mai kyau kuma wasa maras kyau,” inji  Wenger.

LEAVE A REPLY