Hassan Y.A.Malik

Kungiyar kwallon kafa ta Arsenal za ta sake yin nazari akan ragowar kwantiragin mai horas da ‘yan wasanta. Arsene Wenger, da nufin kawo karshen zamansa a kungiyar a matsayin mai horaswa a karshen kakar bana.

Jaridar Sportmail ta rawaito cewa, tuni dai kungiyar Arsenal ta fara tattara sunayen masu horaswa da suke tunanin za su iya zama madadin Arsene Wenger da zarar sun kawo karshen shekaru 22 da Bafaranshen ya yi yana bada karatu a sitediyam din Emirate.

Cikin wadanda sunayensu ke sama-sama akwai: kocin Monaco, Leonardo Jardim, akwai kocin tawagar kwallon kafa ta Jamus, Jaochim Low, sai kocin Celtic, Brendan Rodgers, da kuma mataimakin kocin Manchester Ciy, Mikel Arteta.

Wenger na fuskantar tsananin rashin gamsuwa da yadda ya ke gudanar da kungiyar tun bayan da Arsenal ta sha kashi a hannun Manchester City a ranar Lahadin da ta gabata da ci 3 da nema a gasar Carabao Cup.

Ci gaba da kasancewar Wenger a matsayin kocin Arsenal zai ta’allaka ne akan nasararsa ta kai kungiyar gasar zakarun nahirar turai, kuma a yadda lissafi ke nunawa a halin yanzu, hakan ya ta’allaka ne ga cin kofin gasar Europa League, wanda aka hada kungiyar da AC Milan a wasanni biyu da za buga gida da waje.

LEAVE A REPLY