Daga Abba Ibrahim Wada Gwale

Dan wasan baya na kungiyar kwallon kafa ta Juventus, Giogio Chiellini ya bayyana cewa baiyi mamaki ba da alkalin wasa Machael Oliver yabawa Real Madrid bugun fanareti saboda a cewarsa daman hukumar kwallon kafar nahiyar turai tana nuna musu soyayya.

Juventus dai ta farfado daga kwallaye uku da Real Madrid ta jefa mata a raga a satin daya gabata har gida inda itama taje har filin wasa na Barnabue ta jefa kwallaye uku kafin daga baya alkalin kasa yabawa Real Madrid bugun fanareti kuma su zura kwallon ta hannun dan wasa Cristiano Ronaldo.

Chiellini yace babu mamaki saboda shekarar data gabata Bayern Munchen akayiwa yanzu kuma Juventus ne a alayi saboda haka ba abin mamaki bane tunda daman sun saba da irin wannan alkalancin a baya.

Yace tun daga wasan da suka buga na farko a kasar italiya duk wanda yaga yadda akayi alkalancin wasan yasan akwai abubuwa da dama da bai kamata ace sun faru ba amma saboda wasu dalilai haka suka faru kuma babu yadda suka iya.

Yaci gaba da cewa babu wanda zai yarda cewa zasu iya zura kwallo uku kamar yadda suma aka zura musu amma sunyi kuma sun nunawa duniya cewa sune Juventus kuma sun dora danba zuwa kakar wasa ta gaba.

Real Madrid dai tana neman lashe kofin na zakarun turai karo na uku a jere bayan data kai matakin kusa dana karshe.

LEAVE A REPLY