Daga Hassan Y.A. Malik

Wani sabon bincike na baya-baya nan da manazarta suka gudanar a jami’ar California ya bayyana cewa za a sake samun yanayin nan da a turance ake kira da “grand minimum” nan da shekaru shekaru kadan masu zuwa.

Wannan yanayi na “grand minimum”, yanayi da rana za ta yi sanyi. Ma’ana za ta daina fitar da wannan zafin da ta ke fitawar bisa dabi’a. A maimakon zafi, sai dai ma sanyi da ranar za ta ke saki zuwa ga duniya.

A wani lokaci a baya cikin karni na 17 da aka samu irin wannan yanayi na “grand minimum”, sai da ya daskarar da kogin Thames. Kogin Thames shi e kogi mafi girma a kasar Ingila. Kogin na da tsawon mil 215.

Sai dai, sanyin da ranar za ta ke fitarwa ba iri daya bane a gaba daya fadin duniya. Domin kuwa duk da sanyin da sanyin da ya ke da akwai a yankin turai a lokacin da aka yi wancan na baya, sai da ya kasance akwai yanayi mai dumi a wasu yankuna da suka hada da Alaska da yankin Greenland ta kudu.

A cewar masanan, wannan yanayi na sanyin rana zai taimaka wajen sassauta dumamar yanayi, amma ba zai magance shi ba 100 bisa 100.

Masanan suka ce, yanayin “grand minimum” zai taimaka wajen ragewa duniya zafi da kaso 0.25 a tsakanin shekarar 2020 zuwa 2070.

Wannan bincike dai tuni an wallafa shi a mujallar masana kimiyyar yanayi ta Chicago.

LEAVE A REPLY