Hukumar Yaki Da Safarar Mutane ta kasa (NAPTIP), ta ce ta nemi hadin kan mayu a birnin Benin ta jihar Edo don su taimaka mata wajen yaki da safarar mutane da ya yi kamari a kasar nan.

Darakta Janar ta hukumar, Julie Okah-Donli ce ta bayyana hakan a yayin wani taron kara wa juna sani da hukumar ta gudanar ga ma’aikatanta na Abuja.

Madam Julie ta bayyana cewa, jihar Edo ce ke da mafi yawan mutanen da ake safararsu zuwa turai, kuma bincike ya nuna cewa masu wannan sana’a suna neman taimakon mayu da matsafa kafin su dau hanya.

Wannan ya sanya muka yi kafa da kafa zuwa jihar Edo, kuma muka saka aka tattara mana fitattun mayu da matsafan jihar, inda muka bayyana musu irin halin kuncin da mutanen da ake safararsu zuwa kasashen turai suke samun kansu bayan an kai su an baro.

“Hakika bayaninmu ya kidima mayun, inda nan take suka yi alwashin za su yi aiki da mu wajen kawo karshen fasakaurin mutane daga Nijeriya zuwa kasashen turai.”

Madam Julie ta ci gaba da cewa, “Hukumar NAPTIP za ta ci gaba da kulla kawance da mayu daga sauran sassan Nijeriya, haka kuma za ta karramasu da matsayin JAKADUN HUKUMAR NAPTIP na yaki da safarar mutane.”

“Masu safarar mutane na aiki da matsafa da mayu ne wajen dolantawa mutanen da za a yi safararsu shiga yarjejeniyar mika wuya. Matsafan ne ke yin amfani da fitsarin mutanen da za a yi safararsu, da gashin al’aurarsu, faratansu, da gashin idonsu, da jinin al’adarsu da kuma dan kanfansu. Da wadannan abubuwa ne za a kafe mutanen kuma a rufe bakinsu kuma su mika wuya babu ji babu gani.”

“Bayan kulla an kaddamar da mutumin da za a yi safarar ne matsafin zai fada masa wannan alaka da ta kullu tsakaninsa da mai safarar, alaka ce da ba za ta taba warwaru ba. Alaka ce ta zallar biya irinta ‘Yi-Na-Yi, Bari-Na-Bari,” inji Madam Julie.

Shugabar ta yi alwashin kawo karshen wannan mummunar dabi’a ta safarar mutane da ke nema ta zama ruwan dare a fadin kasar nan.

LEAVE A REPLY