An shirya yin wani kasaitaccen bikin baja kolin wasu hotunan tsiraici na shararren mawakin turancin nan dan kasar Amurka, Tupac Shakur, tare da takardar shaidar mutuwarsa. hotunan dai su ne irin na farko, wanda suke bayyanar da tsiraicin marigayi TuPac da za a kada musu gwanjo.

Ana sa ran kudin da za ayi Gwanjon hotunan zai fara daga $15,000 zuwa abinda ya sauka, kuma za ayi wannan kada gwanjo ne a wani dandali mai suna “Gotta Have Rock and Roll”.

Su dai wadannan hotunan, rohotanni sun ce, wata tsohuwar budurwar marigayi Tupac ce ta taba daukansu da kyamarar daukar hoto, kuma taki bayyanar da hotunan tun a lokacin da ta dauke su, sai a yanzu tace za’a kada musu gwanjo.

Budurar ta bayyana yadda aka yi ta dauki wadannan hotunainda tace “Na dauki wadannan hotunan na tsiraicin marigayi Tupac ne a shekarar 1990 a wani gidan rawa a unguwar Marin County. Ya kasance yana da wata dabi’a (Tupac) duk lokacin da yaje gidan rawa bayan an gama cashiya, yakan baiwa abokansa dariya, ta hanyar kwabe wandonsa na ciki (kamfai) inda yake nuna musu tsiraicinsa su kuma su bushe da dariya”

“A lokacin da abin ya faru, wani dare ne da ba zan manta shi ba, ina kokarin kashe kyamarata da nake daukar hoto a lokacin, sai ga Tupac Shakur ya shigo, kamar yadda ya saba, kawai ya kwabe wandonsa na ciki, ya tsaya zindir, ni kuma nace masa yayi sauri ya kauce ko na dauki hotonsa tsirara, kawai sai yayi min gwalo, ni kuma kawai na dauke shi hakan zigidir”

“Fitilar kyamarata a lokacin ta haska Tupac a lokacin da na dauke shi hoton, alamar da saninsa na dauki hoton amma kuma bai damu ba, ya nuna ko a jikinsa dan na dauki hotonsa tsirara. Hoton dai ya nuna zallar tsiraicin Tupac, daman kuma shi mutum ne mai al’adar cire riga a ko da yaushe”

“Tun a wancan lokaci, babu wanda na taba nunawa wadannan hotuna da na dauki Tupac Shakur zigidir, sai yanzu da nake son a kada musu gwanjo domin a saida su, ta kara da cewar, wadannan hotunan su ne irinsu na farko da za a kada musu gwanjo, domin duk duniya babu wani wanda yake da irin wannan hoto sai ni” a cewar tsohuwar budurwar Tupac wadda ta nemi a sakaya sunanta.

Bayan haka kuma, za a kadawa takardar shaidar mutuwar Tupac gwanjo, wadda a baya an sha yin takadda kan ainihin rasuwar Tupac, ta yadda suke ke musun cewar bai mutu ba. Takardar shaidar mutuwarsa dai an yi ta ne a shekarar 1996, sannan kuma za’a kada mata gwanjon daga $5,000 zuwa abinda ya sauwaka.

Ikon Allah, ko me zaku ce kan wannan batu?

LEAVE A REPLY