Daga Hassan Y.A. Malik

Wata kwararriya akan harkar lafiya, Misis Helen Bulu, ta gargadi iyaye mata a Nijeriya da su guji yi wa sabban jarirai wanka da ruwan zafi da kuma al’adar nan ta fizgar hannu da kafafun jarirai da ake yi da nufin yi musu mika.

Misis Helen da ke aiki da Family Health Clinic a Abuja ta bayar da wannan shawara ce a wajen wani taron wayar da kan mata kan allurar riga kafi da ka yi wa masu goyon ciki da goyon jarirai a Abuja, yau Alhamis.

Ta ci gaba da cewa wannan dabi’a ta yi wa jarirai wanka da ruwan zafi da kuma kokarin yi musu mika ta hanyar jan hannaye da kafafunsu, ba wani abu bane face ‘Afirkance’ kawai, domin kuwa yin hakan bashi da wata alaka da kimiyyar kiwon lafiya.

“Duk wani dumi da jariri ya ke da bukata ya same shi a cikin uwa, saboda haka babu abinda yin wanka da ruwan zafi ke jawo wa jariri sai zafafa yanayin dumin jikinsa daga yanayi na daidai yadda jiki ke bukata zuwa yanayi na zafin da ya wuce kima,” inji Misis Helen.

Helen ta ci gaba da cewa, turawa basa gasa ‘ya’yansu da ruwan zafi kuma basa kokarin yi musu mika kuma yaransu na tashi cikin koshin lafiya.

Sai dai ta ja hankalin iyaye mata da su yi kokarin shayar da jaririnsu da nono babu kakkautawa, domin ruwan nono na taimakawa wajen yin kasa da zafin jikin jariri.

Ta kuma ja kunnen iyaye da su guji yin amfani da ruwan zafi ko shafawa jariri man zafi idan wani bangare na jikina ya kumbura. “Idan kumburi ya faru a jikin jariri, to kar a shafa komai, ki ci gaba da sanya ido a wajen da kumburin ya ke, za ki ga ya sace da kansa bayan wani lokaci.”

“Haka kuma idan zafin jiki ne ya tsananta a jikin jariri kuma aka ga bai yi sauki bayan tsawon lokaci, to sai a ziyarci asibiti don gnin likita, domin babu shakka wannan na nufin akwai zazzabi a jikin jaririn.”

Misis Helen ta ci gaba da jan hankalin mata da su yi kokari su nemi jami’an lafiya don tabbatar da cewa sun shiga tsarin takaita iyali daga makonni 6 bayan haihuwa, domin hakan ne zai bawa mai gida damar kusantar iyalinsa ba tare da tsoron za ta dauki ciki akan jaririn da ke hannunta ba.

Ta kuma yi kira da masu jego da su tabbata sun shayar da jariransu da ruwan nono kadai har na tsawon watanni 6 na farkon rayuwarsu ba tare da basu ko da ruwan sha ba.

Bayan wata shida kuma, sai Misis Helen ta shawarci da a gwadawa jariri koko da manja, domin manja na dauke da bitamin A, wanda ke da amafani wajen girman yara.

LEAVE A REPLY