Daga Hassan Y.A. Malik

‘Yan sandan kasar Indiya sun cafke wata fitacciyar jarumar masana’antar shirya finafinai ta kasar Indiya da ta fito daga yankin kudancin kasar a yankin Tamil Nadu sakamakon samunta da laifin kafa gidan karuwai

Sangeetha Balan mai shekaru 41 ta shiga hannun ‘yan sanda ne bayan da suka yi wa gidanta da ke a Chennai dirar mikiya, suka kuma kamata tare da wani namiji mai suna Sathish, a cewar ‘yan sandan a jiya Litinin.

Zargin na Sangeetha ya fara ne bayan da ‘yan sanda suka kai farmaki wani gidan nishadi na Panaiyur da ke a bayan garin Chennai bayan da ‘yan sandan suka samu bayanan sirri kan ayyukan karuwanci da ake gudanarwa a gidan shakatawan.

Wani jami’in dan sanda ya bayyana yadda suka samu wasu ‘yan mata 4 masu kananan shekaru a gidan shakatawa na Panaiyur wadanda suka ce jaruma Sangeetha ce ta ja ra’ayinsu shiga harkokin karuwanci.

Wani bincike na ‘yan sanda ya bayyana yadda Sangeetha da abokin shashancinta, Sathish ke yaudarar ‘yan mata suna saka su a harkar karuwanci, inda suke yi musu romon baka da cewa wai za su saka su a fim din yankin Tamil.

Tuni dai aka mika ‘yan matan 4 zuwa gidan gyara dabi’a, kuma a nan ana ci gaba da bincike kafin gurfanar da wadanda a ke zargi a gaban kuliya.

An gano cewa dai Sangeetha ta taba fadawa harkar karuwanci kafin ta fara shirin fim a shekarar 1996, inda ta fara da wani fim da ya samu karbuwa matuka wato ‘Karappu Roja’.

Jarumar ta yi fice a wasu shirye-shirye ba talabijin da suka hada da: VANI RANI, CHELLAMAY AVAL da kuma VALLI.

LEAVE A REPLY