Daga Habu Dan Sarki
Wani binciken kwakwaf da jaridar TheCable ta gudanar ya bankado yadda wani maigadi a Kwalejin Tarayya ta ‘Yan Mata (FGGC) dake garin Langtang a jihar Filato yake karbar cin hancin naira dubu 5 domin kulla alakar lalata tsakanin dalibai mata da ke karatu a kwalejin, don su je su kwana da maza a waje.
Wannan maigadi da rahotanni suka nuna cewa, a baya yana aiki ne bangaren dafa abinci amma aka canza masa wajen aiki zuwa bakin kofar shiga makarantar bayan an kama shi da laifin yi wa wata daliba ciki, ya shiga wannan harka ne sakamakon alakar da ke tsakanin sa da wasu ‘yan mata a makarantar, inda yake karbar cin hanci da bai wa daliban kudin mota zuwa inda ake jiransu.
Binciken ya gano cewa ban da wannan maigadi da ke hada baki da bakin maza a waje yana fitar da ‘yan mata, akwai kuma wasu malamai a makarantar wadanda su ma ake zargi da amfani da ‘yam matan ta hanyar da ba ta dace ba.
Dan jaridar TheCable da ya gudanar da wannan bincike ya ji ta bakin wasu daliban makarantar da suka koka da irin halayyar banza da wasu malamai da aka sakaya sunayen su, suke  nuna musu, musamman idan sun shiga ofisoshin su ki kuma sun aike su gidajensu.
Binciken ya gano makarantar  ta FGGC Langtang na fama da matsaloli na rashin katanga mai tsayi da za ta kebe daliban daga dakunan kwanan su, da samar da kyakkyawan tsaro, ta yadda za a kare kimar wannan makaranta da mutuncin wadannan ‘yan mata.
Kokarin da aka yi na ankarar da mahukunta a makarantar da hukumomin ma’aikatar ilimi ta tarayya ya ci tura, yayin da suka nemi a aika musu da koke a rubuce dauke da hujjoji  gamsassu game da abubuwan da ake zargi.
Menene ra’ayin ku game da muhimmancin samar da tsaro a makarantun kwana da daukar mutane nagari aiki, don kula da amanar yaran da ake tura wa karatu nesa da iyayensu.

LEAVE A REPLY