Daga Salisu Abdul Salisu Da Anas Saminu Ja’en
    …Shi ne ya kawo karar mutanan da suka damfare shi ida ya rubuto cewar
“Ina ƙarar wani mai Suna Bala Dan Mallam, Kulu Bashir da kuma Bashir Falau inda suka haɗa kai, suka yaudare ni, kuma suka karɓe mini kuɗaɗe kusan Naira dubu 780, Katin waya na Naira dubu 125, Turare da Atamfofi na kusan Naira dubu 230.
Asali,  mu hadu dasu shi Bala Ɗan Mallam ne ta hanyar Facebook inda ya bude asusu da sunan Mace “Ummi Mansura” inda kuma daga baya muke chart ta hanyar WhasApp, har kuma soyayya ta kullu tsakanin mu, duk da bamu taɓa ganin juna ba. Yayi ta turo mini da hotunan Mace, waɗanda suka sanya na ɗauka da gaske Mace ce, sai da tafiya tayi nisa ne na bukaci mu haɗu amma abin ya gagara. Ya samu ita Kulu ne, ya kuma tsara da ita take yi masa Muryar Mace, sannan shi kuma Bashir Falalu shi ne wanda yake ɗauko hotunan Yayar sa, wadda tuni tayi aure a Kasar waje, yake bawa shi Dan Mallam ɗin, wanda shi kuma yake turo mini dasu a zuwan hotunan Ummi ɗin ne. Ban iya gane cuta ta suke yi ba har sai dana turawa wata Yaya ta irin waɗannan hotuna da sunan taga hoton Matar da nake son aura, sannan ne muka gane ashe duk yaudara ta suke yi. Domin ita Yayar tawa tare suka yi karatu da ainihin ita mai wannan hotuna a Kasar Malaysia.
Bayan na gane cewar damfarata aka yi she ne yasa na kai kara zuwa wurin ‘yan sanda to daga nan ne jami’an tsaron suka dukufa bincike ta hanyar wannan charting din da muka yi da lambar wayar WhatsApp din, kuma cikin ikon Allah yasa bayan kammala bincike da jami’an tsaro ne sai aka tura mu zuwa kotu daga nan ne aka fara yin shari’a da ni da wadannan mutanan inda akai ta yin shari’ar tsawon kusan rabin shekara muna zuwa kotu da su.
Kuma kudirin da na shigar shi ne rokon wannan kotu mai adalci data bi mini hakkina, ta sanya su, su dawo mini da dukkanin abubuwan da suka karɓa daga waje na dan hakan ce zata saka su yi karatun ta nutsu, cikin ikon Allah wannan kotun ta karbo min hakki na daga wurin wadannan mutanan kuma aka daure su tare da hukunta su da dauri ko kuma tara.
Da haka ne nake kira da ‘yan uwa masu amfani da shafukan sada zumunta irin su Facebook, WhatsApp da sauran su da su yi taka tsantsan da sanin irin mutanan da zasu yi mu’amulla da su, saboda wannan lamarin da ya faru da ni ya kamata ya zamarwa mutane izina, Allah ya kara kare mu.

LEAVE A REPLY