Daga Hassan Y.A. Malik

Wani magidanci ya bar harabar kotu cikin hawaye bayan da ya bukaci kotun ta raba aurensa da matarsa mai shekaru 30, wacce ya fadawa kotun cewa kyawun matar tasa ya yi yawa.

A cewar mutumin mai suna Arnold Masuka, kyan matar tasa mai suna Hilda Mleya ya hana shi samun kwanciyar hankali da jin dadin rayuwa.

Ya ce lamarin har sai da ta kai ga ya na tsoron tafiya aiki ko barin ta ita kadai gudun kar ta ja hankalin wasu mazan.

Alkalin kotun da ke zama a Goke a kasar Zimbabwe, Cif Chireya ya tambayi mutumin in da gaske ya ke ya yanke hukuncin sakin matar tasa, duk da cewa su na da kananan ‘ya’ya tare da ita.

Ya kuma roki ma’auratan da su da ci gaba da zama a matsayin mata da miji, amma Masuka ya kekasa kasa ya ce shi fa sam, tun kafin su je kotun ma auren su ya zo karshe.

LEAVE A REPLY