Birin da ya cinye Naira Miliyan 70

Yau a majalisar Dattawa an yi karambatta, inda aka cire Sanata Abdullahi Adamu daga jihar Nassarawa, an cire daga mukamin Shugaban kungiyar Sanatocin Arewa, inda aka maye gurbinsa da Sanata Aliyu Wamakko daga jihar Sakkwato.

Sanata mai wakiltar Kaduna ta tsakiya ya shaidawa manema labarai cewar, sun cire Sanata Abdullahi Adamu ne daga Shugabancin kungiyar, sabida sakaci da yayi har birrai suka cinye kudaden Sanatocin dake kungiyar har Naira Miliyan 70.

Sanata Sani, ya bayyana cewar, bayanai sun same su kan cewar, kudaden da aka ajiye su a gonar Sanatan, wasu birrai sun biyo dare sun cinye su, a sabida haka suka sauke Sanatan daga mukaminsa.

LEAVE A REPLY