Jarman Sakkwato, Alhaji Ummarun Kwabo AA

accen attajiri dan kuwasu kuma Basarake, Jarman Sakkwato Alhaji Ummarun Kwabo AA, a karshen makon da ya gabata, ya bayyana cewar, zai aurar da samari 100 a jihar Sakkwato. Jarman na Sakkwato ya bayyana hakan ne a lokacin day a sshirya wata adduah ta musamman a gidansa.

Yace ya dauki gabarar wannan aniya ne domin taimakawa matasan da suke son yin aure amman bas u da hali. Ya kuma kara da cewar, yana fatan yin wannan hidima domin bayar da tasa gudunmawar wajen yiwa al’ummah hidima, kuma hakan zai rage adadin yawan matasan da suke zaune babu aure babu sana’a.

Alhaji Ummarun Kwabo AA, yace, zai dauki nauyi da dawainiyar yin auren mutum 100 baki daya shi kadai. Biyan sadaki, dinka sabbin suture ga kowanne ma’aurata da kayan daki da kuma duk abinda za’a ci.

Haka kuma, Jarman yace, umarni ne da addininMusulunci yaii domin mawadata irinsa su taimakawa talakawa da kuma raunana. Yace, “Na lura da yadda matasa da yawa suke son yin aure, amma sabida halin yau sun kasa yi, a sabida haka ni na dauki aniyar yi musu aure ko nawa zan kasha”

A lokacin da yake nuna godiya, Tsohon Sakataren Gwamnatin jihar Sakkwato Alhaji Muhammadu Maigari Dingyadi, ya yabawa Jarman Sakkwato, da cewar wannan abu da yayi, yazo a lokacin day a dace, kuma koyi ne da addinin Musulunci, wajen taimakawa masu karamin karfi.

 

LEAVE A REPLY