Ayaba

Kowace ayaba kwaya daya, mai kyau, na dauke da sinadarin bitamin C da bitamin B6. Wannan na nufin a duk lokacin da ka ci lafiyayyiyar ayaba kwaya daya mai matsakacin girma, za ta baka kaso 15 cikin 100 na sinadarin bitamin C da jikinka ya ke bukata a kowace rana, haka kuma za ta baka kaso 33 cikin 100 na sinadarin bitamin B6 dsa jiki ke bukata a kullu-yaumin.

Ayaba na dauke da tarin sinadarin fatashiyam (potassium) wanda ke taimakawa sassan jiki kamar su zuciya da koda su gudanar da ayyukansu yadda ya kamata. Haka kuma ayaba dan itaciya ne da ke bawa jiki sinadarin faiba (fiber) wadatacce. Sinadarin faiba na daidaita al’amuran ciki wajen takaita ko hana kumburinsa da lalacewarsa, wanda hakan ke hana kumburin ciki, yawan gudawa ko rashin  samun ba-haya a kan kari.

Ga wasu abubuwa 11 da ayaba ke yi ga lafiyarmu wajen ingantata:

 1. Ayaba na taimakawa wajen rage kiba maras misali
 2. Ayaba na magance cutar gyambon ciki (ulcer)
 3. Ayaba na magance kananan matsalolin da ke da alaka da koda
 4. Ana amfani da ayaba wajen neman kiba ga wadanda suke fama da rama
 5. Ayaba na taimakawa mata wajen ciwon da suke fama da shi a lokacin al’ada
 6. Ayaba na gyara al’amuran ciki musamman ga wadanda ke fama da taurin ba-haya
 7. Ayaba na magance ciwon basir
 8. Ayaba na taimakawa wajen daidaita adadin sikarin da ke cikin jini musamman ga masu ciwon sikari
 9. Ayaba na magance ciwon gabobi da ke kama manya da yara
 10. Ayaba na gyara lafiyar ido da kaifafa gani
 11. Ayaba na kwarara kashi

 

Har ila yau, sinadarin fatashiyam da ke cikin ayaba na taimakawa wajen bude hanyoyin jini da daidaita gudun jinin. Wannan ko shakka babu yana rage hatsarin kamuwa da ciwon zuciya da dangoginsa.

LEAVE A REPLY