Na'urar da zata taimakawa mutum ya kashe kansa

An kirkiro wata na’ura da aka yi da kimiyyar 3D wacce aka sa ma suna Sarco wanda mutum zai iya amfani da na’urar domin ya kashe kansa nan take. An baje wannan kimiyyar ne a wajen wani jana’iza a garin Amsterdam.

Philip Nitshke wanda aka fi sani da Likitan mutwa (Dr Death) shi ne ya gabatar da na’urar na 3D ranar Asabar 14 ga watan Aprilu na 2018.

Wannan kimiyyar hadin guiwa ne tsakanin Dr Philip Nitschke da dan kasar Dutch injiniya Alexander Bannink.

Mutanen biyu suna da muradin ganin sun wadatar da wannan na’ura a fadin Duniya wanda zai yi aiki ta hanyar hana iskar oxygen lamari da zai kai ga mutuwar dan adam.

Isyaku.com

LEAVE A REPLY