Untethered astronaut above Earth (Digital Composite)

Najeriya ta bayyana shirye shiryenta na tura mutum zuwa sararin subahana, da aka fi sani da duniyar wata nan da zuwa shekarar 2030. A kokarinta na tafiya kafada da kafada da sauran kasashen duniya, Najeriya ta bayyana cewar shirye shirye suna kankama kan wannan batu.

Ministan kimiyya da fasaha na kasa Dr. Ogbonnaya Onu ne ya sanar da haka a birnin tarayya Abuja. Ministan yace, jami’an hukumar lura da sararin samaniya ta kasa, zasu ziyarci takwarorinsu na kasar Chana domin tattauna muhimman al’amura suka shafi sararin samaniya da kuma, samun ilimi kan yadda abun yake.

Sai dai a lokacin da Ministan yake bayar da wannan tabbaci, mutanan da suke sauraren jawabinsa, sun rude da sowa, suna fadin wannan batu ba mai yuwuwa bane. Mutane da dama dake wajen sun dinga raha da junansu, suna fadin ai kam da kamar wuya.

A wajen mutane suka dinga tattauna, batun tauraron dan Adam da Najeriya ta taba harbawa sararin samniya inda Gwamnati ta bayar da sanarwar cewar Tauraron ya bace a sararin saminya, bayan kuma an gama kashe dalar Amurka miliyan 3 domin tura Tauraron.

Bayan da jama’a suka  yi shiru ne,sai Ministan yace, “ina mai tabbatarwa da jama’a cewar wannan batu na tura mutum zuwa sararin samaniya ba abin dariya bane, da gaske Najeriya take, kuma zata yi dukkan mai wuyuwuwa wajen ganin ta cimma wannan buri”.

Yaya kuke kallon wannan batu? Shin zai iya yuwuwa kuwa?

LEAVE A REPLY