Daga Hassan Y.A. Malik

A wani lamari da ka iya kawo wa wannan sabuwar kimiyya koma baya, daya daga cikin motocin da aka kirkira masu tuka kan su ta kade wata mata akan titi a garin Arizona da ke kasar Amurka.

Motar mallakar kamfanin Uber ta kade matar ne a yayin da take tukin gwaji a ranar Lahadin da ta gabata. Dama dai motocin a yanzu haka su na fuskantar gwaji ne a jahohin Arizona, Pittsburg da Toronta.

An sha fadin cewa kimiyyar da motocin da zo da su zai rage faruwar hadura da kashe-kashe akan titina, toh sai dai faruwar wannan lamari ka iya sanyawa a musanta wannan batu.

A bisa faruwar wannan lamari, kamfanin ya ce zai dakatar da gwaji a yankin Arewacin Amurka zuwa nan gaba duk da cewa majalisar kasar Amurka ta dade ta na tattaunawa game da kafa dokar da za ta gaggauta fara amfani da motoci masu tuka kan su.

Rahotanni sun bayyana cewa matar da aka kade, Elaine Herzberg mai shekaru 49 na kan keke ne a lokacin da abun ya faru da misalin karfe 10 na dare. Motar na tafiya ne akan gudun kilomita 65 a kowanni awa a lokacin.

Toh sai dai wasu rahotannin sun nuna cewa ba laifin motar ba ne domin kuwa ko da a ce direba ke tuka ta, da ba za a iya magance faruwar hakan ba duba da yadda matar da shigo titin da sauri ba tare da an ganta ba.

LEAVE A REPLY