Daga Hassan Y.A. Malik

Wani bincike na baya-bayan nan da jami’ar Cambridge ta fitar ya bayyana cewa akalla kaso 40 cikin 100 na  mata masu ‘ya’ya 5 ko fiye na da barazanar kamuwa da ciwon zuciya sama da masu ‘ya’ya 1 ko 2.

Binciken da manazarta suka fitar a jiya Litinin ya bayyana yadda kaso 25 na iyaye mata masu adadin ‘ya’ya 5 zuwa sama ke cikin hatsarin kamuwa da mutuwar barin jiki, inda kaso 17 kuma ke cikin hatsarin kasawar zuciya.

Dakta Clare Oliver-Williams, wanda shi ne ya jagoranci nazarin ya ce: “Mun san cewa yana da matukar wahala uwa ta iya kulawa da lafiyarta yadda ya kamata in tana da yara da yawa.”

Gidauniyar lafiyar zuciya ce ta dauki nauyin gudanar da binciken da aka yi akan mata 8,000 daga yankin turai da bakaken mata ‘yan Amurka masu shekaru tsakanin 45 zuwa 64.

An gabatar da sakamakon binciken ne a wajen taron kungiyar masana lafiyar zuciya ta Burtaniya a garin Manchester da ke a kasar Ingila.

Image result for Large family

 

 

LEAVE A REPLY