Daga Hassan Y.A. Malik

‘Yan sanda a jihar Gombe, a jiya Talata sun gurfanar da wani uba mai shekaru 50 da haihuwa da aka bayyana sunansa da Sama’ila Zakari a gaban kotun majistare bisa zarginsa da laifin yin fyade ga ‘yarsa mai shekaru 15 da haihuwa, lamarin da ya kai ta ga samun juna biyu.

Rahoton karar ya bayyana cewa wanda a ke zargi dan asalin garin Deba ne da ke karamar hukumar Yamaltu/Deba kuma ya aikata laifin da a ke zarginsa ne a ranekun 2 da 8 ga watan Mayu.

Mai shigar da karar ya fadawa kotu cewa, a wadannan raneku biyu da aka fada, wanda a ke zargi ya ciccibi ‘yarsa zuwa dakinsa na kwana da misalin karfe 10:00 na dare, inda ya yi lalata da ita ba tare da son ta ba.

Mai shigar da karar ya tabbatarwa da kotu cewa a yanzu dai yarinyar na dauke da cikin wata 2 na mahaifinta.

Mai shigar da karar ya ci gaba da cewa an gurfanar da Sama’ila Zakari bisa laifukan aikata lalata da dan uwa na jiki da kuma fyade, laifukan da suka ci karo da tsarin dokar kundin Penal Code sashe na 390 da 282.

Sai dai shi wanda a ke zargi ya ki amsa laifin da a ke zarginsa da su a gaban mai shari’a Dorabo Sikam.
Mai shigar da kara, Sufeta Baba Shekari ya bukaci kotu da ta daga sauraren karar don ‘yan sanda su kammala bincike tare da kawo wa kotu shaidu.

Kotu ta dage karar zuwa ranar 21 ga watan Mayu tare da umarnin a garkame Sama’ila Zakari har zuwa ranar da za ta ci gaba da sauraren karar.

LEAVE A REPLY