Ali Al-Qaisi dauke da sabon jaririn da aka haifa masa

Wasu ma’aurata a birnin Tabuk na kasar Saudiyya sun samu karuwa. Ali Al-Qaisi dan shekaru 16 ya samu karuwar da namiji. Al-Qaisi shi ne uba mafi karancin shekaru a kasar Saudiyya, ma’auratan wadan da suka fito daga birnin Tabuka na kasar ta saudiyya, sunyi aure ne kimanin Shekara daya da rabi da ta gabata.

Al-Qaisi yana cikin shekara ta biyu a karamar sakandire aka yi masa aure. Wannan aure dai ya jnayo cece kuce da yawa a kasar ta Saudiyya tsakanin masu goyon baya da wadan da suke bayyana adawarsu da aurar da kananan yara.

Masu goyon bayan wannan aure na da ra’ayin matukar ango zai iya sauke nauyin iyali babu wata matsala a auren nasu. Bugu da kari, masu nuna goyon bayan wannan aure na da’awar cewar, irin wannan aure zai katange samari da yawa daga aukawa zina inda ana yinsa.

A gefe guda kuma, masu sukar irin wannan auren na zargin yaran sam basu balaga ba aka aurar da su, wanda a tunaninsu hakan cutar da yaran ne. Domin a cewarsu, ba lallai bane zasu iya daukar wahalar da ke tattare da dawainiyar aure da kuma kula da iyali da sauran bukatun aure.

Ku bayyana mana ra’ayinku kan wannan auren.

LEAVE A REPLY