Ma'aikaciyara Bankin da ta kashe kanta sabida mijinta yana neman mata

Daga Hassan Y.A. Malik

Al’ummar yankin Ughelli ta jihar Delta sun shiga cikin yanayin jimami sakamakon kashe kanta da wata ma’aikaciyar banki da aka bayyana sunanta da Peace Uzezi Akpabaro ta yi sakamakon neme-nemen mata da mijinta ke yi.

Peace mai shekaru 32 da haihuwa, kuma uwa ga ‘ya’ya biyu ta yanke hukuncin kashe kanta don ta huta da takaicin halin rashin kima da mijinta ya ke nunawa na neman mata kamar dai yadda jaridar Vanguard ta rawaito.

Jaridar ta bayyana cewa lamarin ya ta’azzara ne a lokacin da mijin nata ya yanke shawarar dawo da farkarsa cikin gidansu ta zauna da su, lamarin da ya hasala Peace, ta kuma ga cewa da ta rayu da wannan cin fuska gwara ma ta mutu ta huta.

Peace ta yanke hukunci da ta sha maganin kwari ne a ranar Larabar da ta gabata. Kafin mutuwarta, Peace na aiki ne da daya daga cikin bankunan Nijeriya da suka bukaci da a sakaya sunansu da ke da ofishinsa a kan titin kasuwa “Market Road”, Ughelli.

Ko a baya ma dai, sai da Peace ta rabu da mijinta, kafin daga baya ‘yan uwa su daidaita su, ta koma dakin mijinta.

Wata kawar Peace da ta bukaci kar a bayyana sunanta ta bayyana cewa, “An samu gawar Peace ne a kwance a cikin dakinta a daren ranar Laraba bayan ta dawo daga aiki. Ta kasance tana samun matsala da mijinta wanda ya ke da yawan kwashe-kwashen ‘yan mata. A gefen gawar Peace, an samu robar maganin kashe kwari na Sniper da babu komai a cikinsa da kuma wasu kwayoyin magani.”

Wani babban jami’in dan sanda da ke aiki da ofishin ‘yan sanda na Ughelli mai suna Agbarha-Otor, ya tabbatar da faruwar mutuwar Peace, kuma ya bayyana cewa tuni aka kai gawar Peace wajen ajiye gawarwaki, inda ‘yan sanda ke ci gaba da nasu binciken.

LEAVE A REPLY