Stephen Hawking

Fitaccen masanin kimiyyar nan na duniya Stephen Hawking ya rasu yana da shekara 76.

Danginsa sun ce Farfesan ya rasu ne a gidansa da ke garin Cambridge da sanyin safiyar ranar Laraba.

Masanin dan kasar Birtaniya ya yi fice ne saboda aikace-aikacensa kan wani yanki da masana kimiyya ke hasashen cewa duk abin da ya gifta ta wurin zai bace.

Sannan ya rubuta litattafai da dama na kimiyya ciki har da “A Brief History of Time”.

Tun yana dan shekara 22 likitoci suka gano cewa yana fama da wani nau’i na cutar motor neurone wacce ke shafar kwakwalwa da kuma jijiya.

Cutar ta sa shi ba ya iya tafiya sai a keken guragu, sannan ba ya magana sai da taimakon na’ura.

A wata sanarwa da suka fitar, ‘ya’yansa, Lucy da Robert da Tim, sun ce: “Muna cikin matukar bakin ciki cewa mun rasa mahainfinmu abin kaunarmu a yau.

“Kwararren masanin kimiyya ne kuma gwarzo wanda rawar da ya taka za ta ci gaba da wanzuwa a doron kasa nan da shekaru masu tsawo.

Jama’a da dama na ci gaba nuna alhininsu kan rasuwar Farfesa Hawking.

Fira ministar Birtaniya Theresa May ta bayyana shi a matsayin “kwararre kuma gwarzo a cikin gogaggun masana kimiyya na wannan zamani”.

 

BBCHausa.com

LEAVE A REPLY