Daga Bashir Ibrahim Na’iya

A ranar Litinin January 22, 2018 ne babban kamfanin nan na AMAZON ya bude katafaren Kanti mai suna “Amazon go” a garin Seattle, a jihar Washington ta kasar Amurka.
Wannan kanti shi ne na farko a duniya da za ka shiga ka sayi duk abin da ka ke so ka fita salin-alin ba tare da ka bi layin biyan kudin ba, domin babu kashiya, babu cakin wajin fita, babu wani waje ko gurbin da za ka biya kudi, kawai zaka dauki abinda kake so ka fita: “grab and go” kawai ka shiga ka dauki abin da kake so, ka fita kayi tafiyarka ba babu bata lokacin bin layi wajen biya.
Haka kuma, babu bata lokacin “self scan”, wato fayyace kowanne kaya da ka dauka da kanka. Abin da kawai za ka yi shi ne, kana shiga kantin za ka bude jadawalin “app” din “Amazon Go” dake cikin wayarka, shike nan ka gama. Duk abin da ka dauka sai kawai ka sa a cikin jakar idan ka gama ka fita, kana fita idan ka duba wayarka, za ka ga jerin din duk abubuwan da ka dauka, kuma har sun riga sun zare kudin kayan daga daga asusunka na banki.
Image result for Amazon go store
Ku bude link din youtube dake kasa dan ganin yadda abun yake. Ga duk mai son karanta cikakken yadda wannan sabuwar fasahar take, to ku yi searching din “amazon go”.
 Allah Sarki, duniya ta ci gaba, an bar mu a baya, muna ta kashe junan mu.
Image result for Amazon go store
Ku kalli youtube din ga link din nan a kasa:

LEAVE A REPLY