Daga Hassan Y.A. Malik

A wani kudiri da gwamnatin kasar Austria ta fitar a jiya Laraba, gwamnati ta haramtawa yara mata masu zuwa makaratun kafin firamare da makaratun firamare daura kallabi.

“Koyawa yaranmu mata kanana rufe kansu bashi da muhalli a kasarmu,” kamar yadda aka jiyo shugaban gwamnatin kasar Austria, Chancellor Sebastian Kurz na fadawa manema labarai bayan kammala taron a jiya.

A cewar shugaba Sebastian, “Wannan zai kawo karshen nuna wariya da akae nunawa yara mata tare kuma da goge maganar wariyar jinsi a fadin kasar Austria.”

“Yana da matukar muhimmaci mu cire batun nan na siyasar da ke cikin addinin Islam ta yadda ‘ya’yanmu za su tashi ba tare da wani abu na nuna banbamci tsakaninsu da sauran yara ba,” shi ma mataimakin Chancellor, Heinz-Christian Strache na jam’iyyar Freedom Party ya ce.

Zuwa yanzu dai kananan yara mata masu rufe kawunansu da kallabi, adadinsu bashi da wani yawa, sai dai akwai fargabar karuwarsu kamar yadda Chancellor Kurz ya bayyana.

Kimanin rabin shekara da ta gabata ne dai kasat ta Austria ta kafa dokar hana sanya nikabi a fadin kasar. Dokar da zuwa yanzu aka samu akalla mata 50 kacal da saba ta.

Domin tabbatar da wannan kudiri ta haramta daura kallabi ta zama doka, gwamnati na bukatar hadin kan jam’iyyun adawa don samun rinjaye da kaso 2 bisa 3 a majalisa.

Jam’iyyun Social Democrat da Liberals sun nuna sha’awarsu ta narawa kudirin baya, sai dai sun bayyana cewa kudirin na bukatar fadadawa da fayyacewa ta yadda ba zai zama kawai a ce an haramta sanya kallabi ba ne.

LEAVE A REPLY