Hassan Y.A.Malik

Wani matsafi mai matsakaicin shekaru da aka bayyana sunansa da Ogbuebunu, bayan da ya shiga hannun ‘yan kato da gora, ya yi da’awar cewa yana sayen dan kanfai na budurwa wacce bata taba sanin namiji ba akan Naira dubu 10 kowane daya.

‘Yan bijilan ne suka kama Ogbuebunu a karshen makon da ya gabata a kauyen Abagana, cikin karamar hukumar Njikoka, jihar Anambara, bayan da matasa a kauyen suka koka da yadda matsafin ke gudanar da muggan tsibbace-tsibbace a kauyen.

Wani shaidar gani da ido da ya bukaci da kar a bayyana sunansa ya ce, Boka Ogbu ya dauki hayar wani yaro don ya dinga shiga gidaje yana sato masa wandunan ‘yan mata balagaggu da basu taba sanin namiji, kuma yana biyan yaro Naira dubu 10 a kowane kanfai. Sai dai a irin wannan yanayi ne aka kama kam yaron, sanadin da ya sanya aka hankado keyar yaron zuwa inda bokan ya ke aiwatar da tsafinsa.

A lokacin da boka Ogbu ke mayar da zance, ya tabbatar da cewa yana yin amfani da wandunan ‘yan matan ne wajen gudanr da wani tsafi da ke kara masa karfi da kuma yawan masu zuwa neman taimako wajensa.

Ita kuma budurwa da aka yi amfani da wandonta, za ta kamu da wata rashin lafiya da bata jin magani, kuma daga karshe ta mutu.

Da aka tuntubi kakakin ‘yan sanda na jihar Anambara, Nkeiruka Nwode, ta tabbatar da cewa ta samu labarin faruwar lamarin a cikin gari, amma har zuwa lokacin da aka kammala hada labarin nan kes din bai zo gabanta a hukumance ba.

LEAVE A REPLY