Mista Roberto mutumin da yafi kowa girman mazakuta

Jaridar Daily Mail ta kasar Burtaniya ta ruwaito Roberto Esquivel dan asalin kasar Megziko a matsayin mutumin da yafi kowa girman halittar da namiji a duniya. A cewar Jaridar, Mista Roberto yana da halitta mai tsawon inci goma sha tara (19inch) wadda tsawonta yakai tsawon hannun matsakaicin yaro.

Jaridar ta kara da cewar, Gwamnatin kasar ta Megziko ta ayyana Roberto a matsayin wanda yake fama da larura tsawon mazakuta. A cewar hukumomin kasar, wannan tsawon da mazakutarsa ta yi ba na lafiya bane.

Sai dai mutumin yaki yadda da tayin da Gwamnati ta yi masa na cewar za’a rage masa tsawon mazakutarsa idan yana da bukata, amma dai mutumin yace bai gamsu ba.

Mista Roberto dan shekaru 54 yace baya iya yin aiki kuma baya iya sanya tufafin da zasu kare masa al’aura, domin duk kayan da ya sanya sai al’aurarsa ta bayyana sabida girmanta, yace a lokacin da yake yin aiki, da yawan ma’aikata kan bar abinda suke suna kallon al’aurarsa na yawo a cikin wando.

Yanzu dai Gwamnatin kasar Megziko ta ayyana Mista Roberto a matsayin mara lafiya da yake bukatar kulawar hukuma. Yanzu dai Mista Roberto yana samun kulawa ne daga Gwamnatin kasar.

DAILY MAIL

LEAVE A REPLY