Wasu gungun ‘yan kungiyar Asiri ne suka tarwatsa bikin Kirsimeti yau da safe a birnin tarayya Abuja. Matasan da ake kyautata zaton matsafa ne, sun farwa mutane da ababen hawa sun banka musu wuta a Bwari dake birnin tarayya Abuja.

Kiristoci da suke yin ayyukan Ibada a cikin Kanisoshinsu,an gansu suna rugawa a guje domin gudun ceton ransu. Matsafan dai sun tare hanyoyi tare da cinnawa tayoyin mota wuta, inda suka dinga dukan mutane babu ji babu gani.

Wata majiya daga fadar mai martaba Sarkin Bwari ta shaidawa kamfanin dillancin labarai na Najeriya NAN cewar, abin ya faru ne sakamakon kashe wani dan kungiyar matsafan da aka yi a yankin, a ranar lahadi, abinda ya sanya ‘yan kungiyar daukar doka a hannu.

Wani ganau mai suna Jushua ya shaida cewar, yaga gungun matsafan sun nufi fadar mai martaba Sarkin Bwari bayan da suka dinga kunnawa shagunan mutane wuta a kasuwar Bwari.

Tuni dai jami’an tsaron ‘yan sanda da na soji suka shawo kan matsalar. Kakakin rundunar ‘yan sanda ta kasa reshen babban birnn tarayya Abuja Anjuguri Manzah, ya tabbatar da faruwar lamarin, ya kuma ce, rundunar na gudanar da binciken musabbabin faruwar lamarin.

 

LEAVE A REPLY