A group of nudists socialize at the bar before dining together at a "Clothing Optional Dinner" at a New York City restaurant, February 17, 2005. The diners arrived on a cold Thursday night looking remarkably respectable and stripped off scarves, hats and coats. They didn't stop there. Sweaters, shirts, skirts, pants, underwear all end up stashed in a plastic bag by the bar. This is the monthly "Clothing Optional Dinner" for a group of nudists who wanted something a bit more elegant than the wilderness getaways and beach resorts they generally frequent. Around 30 people arrived for the buffet dinner - no hot soup on the menu - most of them middle-aged, several married couples, some singles, the youngest perhaps in their 30s. Health regulations mean staff must remain clothed even if they wanted to join in. And diners must bring something to sit on - a towel or, for discerning women, an elegant silk scarf. FOR RELEASE WITH STORY LIFE-NAKED REUTERS/Mike Segar MS - RTRNR4U

A kasar Faransa an bude wani sabon gidan abinci da mutane zasu dinga zuwa cin abinci zigidir. Sabon gidan abinci mai suna O’naturel an bude shi ne a babban birnin kasar Fari, sabon gidan abincin zai baiwa dangi da iyalai damar zuwa su yi karin kumallo ko cin abincin rana ko cin abin dare.

An dai bude wannan sabon gidan abincin ne a ranar Juma’ar nan da ta gabata, bayan da masu rajin yawo tsirara sukai ta kiraye kirayen a bude shi, domin suje su gwangwaje tare da iyalansu.

Manajan gidan sabon abincin Mista Stephane Saada, ya bayyana jin dadin kan irin yadda jama’a ke tururwa zigidir suna zuwa domin su ci abinci a wajensu. Yace wannan abin da mutane ke yi ya kara musu kwarin guiwa, kuma zasu zage dantse wajen ganin sun hidimtawa mutane.

Haka nan, suma masu makwabtaka da gidan abincin sun nuna jin dadinsu kan yadda aka bude sabon gidan abincin da zai basu damar zuwa cin abinci da iyalansu zigidir.

A wannan gidan abinci, kudin abinci mafi arha shine wanda kudinsa ya kama kudin tarayyar turai (Euro 30) Kimanin Naira 12,420. Jama’a da dama sun bayyana farashin da cewar bai yi tsada ba.

Allah daya gari bamban. Meye ra’ayinku kan wannan batu?

LEAVE A REPLY